Labarai
Majalisar Dattawa a Najeriya ta amince da sababbin hafsoshin tsaron kasar

Majalisar Dattawa a Najeriya ta amince da sababbin hafsoshin tsaron da Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya naɗa ranar Juma’a da ta gabata, bayan sauke tsaffin hafsoshin.
Majalisar dai ta amince da Laftanar Janar Olufemi Oluyede a matsayin babban hafsan tsaro, da kuma Manjo Janar Waidi Sha’ibu a matsayin hafsan sojan ƙasa, sai Rear Admiral Idi Abbas hafsan sojan ruwa, da kuma Air Marshall Kennedy Aneke hafsan sojan sama.
Yayin tantancewar da aka yi musu a yau Laraba, sabbin shugabannin sojan sun amsa wasu tambayoyi daga ‘yanmajalisar bayan gabatar da kan su da tarihin ayyukan da suka gudanar kafin naɗin nasu.
You must be logged in to post a comment Login