Labarai
Majalisar Dattawa a Najeriya ta roki shugaba kasar da ya amince a dauki sabbin sojoji dubu dari

Majalisar Dattawa a Najeriya ta roki shugaba kasar Bola Ahmad Tinubu da ya amince a dauki sabbin sojoji dubu dari domin yakar ta’addanci, ‘yan bindiga da kuma yawaitar sace dalibai a fadin kasar.
Sanatocin sun kuma bukaci a gudanar da cikakken bincike kan yadda aka kashe kudaden shirin Safe School Programme, bayan yawaitar hare-hare kan makarantu duk da kudaden da aka ware don tsaron su.
Bukatar hakan dai na zuwa ne bayan harin da aka kai wa makarantar ‘yan mata ta Maga a Jihar Kebbi, inda aka kashe mataimakin shugaban makarantar tare da sace dalibai 25.
Sanata Adams Oshiomhole ne ya jagoranci tattaunawar, inda ya nemi kara karfin dakarun tsaro da amfani da fasahar zamani wajen bibiyar masu laifi.
Shugaban Majalisar Dattawar sanata Godswill Akpabio, ya goyi bayan shawarwarin, tare da kiran ga gwamnatin tarayya da ta binciki kudaden shirin tsaron makarantu da tabbatar da kariya ga dalibai a yankunan da ke fama da matsalar tsaro.
You must be logged in to post a comment Login