Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan majalisa sun yi Allah wadai da karuwar matsalar tsaro a Najeriya

Published

on

Majalisar wakilai da ta dattijan kasar nan, sun yi Allah  wadai bisa yadda ake samun karuwar matsalar tsaro a kasar.

Majalisun biyu sun bayyana takaicinsu kan yadda aka sace sama da dalibai dari uku a makarantar kimiyya da ke Kankara a jihar Katsina a baya-bayan nan.

Kazalika majalisaun biyu sun ce babu bukatar gayyatar ministan tsaro da sauran hafsoshin tsaron kasar da na hukumar sirri ta DSS kan batun tattauna sace daliban a makon da ya gabata.

A don haka suke bukatar shugaba Buhari da ya gagguta samar da mafita ga me da sha’anin tsaro a Najeriya, musamman a fannin garkuwa da mutane da kuma kashe su.

Shugaban majilsar dattijai Sanata Ahmad Lawan ya ce za su ci gaba da hada kai da dukkanin shugabanni don tabbatar da an kawo karshen matsalar tsaro da ya addabi kasar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!