Labarai
Majalisar Dattawa na shirin tantance Farfesa Joash Amupitan

Ana sa ran Majalisar Dattawa za ta tantance Farfesa, Joash Ojo Amupitan domin zama sabon shugaban hukumar zaɓen ƙasar INEC yau Alhamis.
Matakin na zuwa ne bayan da Shugaba Tinubu ya aike wa majalisar wasiƙar buƙatar tantance shi.
A makon da ya gabata ne dai majalisar ƙasa ta amince da naɗin Farfesa Amupitan a matsayin wanda zai jagoranci hukumar zaɓen ƙasar.
Bayan tantancewa da amincewar majalisar dattawan, Shugaba Tinubu zai rantsar da shi a matsayin shugaban hukumar da ke kula da shirya zaɓukan ƙasar.
A dai makon da ya gabata ne tsohon shugaban hukumar, Farfesa Mahmud Yakubu ya sauka daga muƙamin bayan ƙarewar wa’adin sa.
You must be logged in to post a comment Login