Labarai
Majalisar Dattawa ta Dakatar da muhawarar gyaran dokar zaɓe

Majalisar Dattawan kasar nan ta dakatar da muhawarar gyaran Dokar Zaɓe, inda ta yanke shawarar shiga tattaunawar sirri a bayan fage kafin ɗaukar matsaya ta ƙarshe.
Shugabannin Majalisar sun bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne domin bai wa ‘yan majalisar damar nazari mai zurfi kan ƙudirin gyaran dokar, tare da tattaunawa a tsakaninsu ba tare da matsin lamba ba.
A cewar Majalisar, manufar dakatar da muhawarar ita ce kauce wa yin gaggawa wajen yanke hukunci kan dokar da ke da matuƙar muhimmanci ga tsarin dimokuraɗiyyar ƙasar nan, musamman yadda za ta shafi zaɓe da sahihancinsu.
Majalisar ta ce za ta dawo kan batun ne bayan kammala tattaunawar sirrin da kuma samun fahimta ɗaya a kan muhimman sassa na gyaran dokar.
You must be logged in to post a comment Login