Connect with us

Labarai

Majalisar Dattawa ta fara gyaran kundin tsarin mulkin kasa na 1999

Published

on

Majalisar Dattawa ta kasa  ta fara daukar matakan gyara kundin tsarin mulki na shekarar 1999 domin kara kaso na kudaden shiga da Gwamnatin Tarayya ke samu daga Asusun Tarayyar. Majalisar ta ce tsarin rabon kudaden da ake amfani da shi a yanzu bai dace da yawan nauyin al’umma da ke kan gwamnatin ba, musamman a fannin tsaro da sauran ayyukan more rayuwa.

 

Gwamnatin Tarayya dai na karbar kashi 52.68, yayin da jihohi 36 ke karbar kashi 26.72, sannan kananan hukumomi 774 ke samun kashi 20.60 na kudaden shiga. 

 

Duk da haka, kudirin da Sanata Sunday Karimi na Kogi ta Yamma ya gabatar ya nemi a kara wa Gwamnatin Tarayya kaso, yana mai cewa tsarin da ake da shi ya tsufa kuma ba ya iya daukar nauyin ayyukan kasa.

 

Sanata Karimi ya bayyana cewa karancin kudi na shafar gyaran hanyoyin  da kuma yaki da ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a sassan kasar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!