Kiwon Lafiya
Majalisar dattawa ta musanta kalaman shugaban ma’aikata, kan batun gaza biyan bashin dillalan man fetur
Majalisar dattawa ta musanta kalaman da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari ya yi na cewa, majalisun dokokin tarayya ne musabbabin gaza biyan dillalan mai bashin da suke bin gwamnati.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun majalisar dattawa Sanata Aliyu Sabi-Abdullahi ya fitar jiya a Abuja.
Sanarwar ta kuma ruwaito shugaban kwamitin yada labaran majalisar na musanta cewa, su suka janyo tsaiko ga shirin biyan bashin da dillalan man suke bin gwamnatin tarayya, a cewar sa babu kashin gaskiya cikin kalaman na Abba Kyari.
Sanata Aliyu Sabi-Abdullahi ta cikin sanarwar ya kara da cewa babu wani lokaci da aka turo wa majalisar dattawa da batun biyan dillalan mai bashi da suke bin gwamnatin tarayya domin su a iya saninsu gwamnati ta cire tallafin mai.
Sanarwar ta ce daga cikin dillalan mai da suka halarci ganawa da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar Abba Kyari sun yi ta kiran wasu daga cikin mambobin majalisar dattawa kan batun, lamarin da ya sa majalisar ta ga da cewar ta yi karin haske kan lamarin domin ta wanke kan ta.