Labarai
Majalisar Dattawa ta neman a yi dokar hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane

Majalisar Dattawan Najeriya ta bukaci da a kafa dokar zartar da hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin yin garkuwa da mutane da kuma manyan laifukan ta’addanci, ba tare da zabin biyan tara ba.
Majalisar ta bukaci a gaggauta gyara dokar ta’addancin ne domin aiwatar da wannan sauyi.
Haka kuma ta neman Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake fasalin tsarin tsaro domin samun ingantaccen sakamako, tare da tabbatar da goyon bayan ta a yunkurin shawo kan matsalar rashin tsaro.
Majalisar ta kuma rushe kwamitocin tsaro na din-din-din da Kwamitin tsaro da leken Asiri da kuma Kwamitin Rundunar Sojin Saman Najeriya, inda tace za a sake kafa wasu nan gaba kadai.
You must be logged in to post a comment Login