Connect with us

Labarai

Majalisar Dattawa ta rage kwanakin da ta sanar na zaben badi

Published

on

Majalisar Dattawa ta rage kwanakin da ta sanar na zabe zuwa 300 domin kauce wa cin karo da Ibadar Azumin badi.

‎Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da gyaran sashe na 28 na kudirin dokar zabe ta shekarar 2026 inda ta rage adadin kwanakin sanar da zaben gama-gari daga kwanaki 360 zuwa kwanaki 300.

‎Rahotanni sun ce an yi wannan gyara ne domin tabbatar da cewa zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya na shekarar 2027 ba su zo daidai da watan azumin Ramadan ba.

‎Tun da farko majalisar ta amince da kudirin da sharadin kwanaki 360, sai dai daga bisani ta janye wancan mataki tare da mayar da kudirin gaban kwamitin majalisa domin sake duba shi.

‎Gyaran dai na nufin ba wa INEC karin sassauci wajen tsara ranakun zabe, tare da la’akari da yanayin addini da zamantakewa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!