Kiwon Lafiya
Majalisar dattawa ta zargi kamfanin NNPC da dillalan man fetur wajen karancin man fetur
Majalisar dattawa ta zargi Kamfanin mai na kasa NNPC da kuma dillalan man fetur da hannu wajen janyo karancin man fetur a kasar nan.
Shuagban kwamitin da ke sanya ido kan al’amuran man fetru na majalisar Kabiru Marafa ne ya bayyana hakan jiya, yayin wani rangadin duba irin halin da rashin man ya haifar a kasar nan, a Gusau.
Kabiru Marafa wanda ya samu rakiyar daya daga cikin mambobin kwamitin Abdullahi Danbaba, ya bayyana cewa, rangadin na daga cikin aikin da shugaban majalisar ya sanya kwamitin yayi na gudanar da binciken abinda ya sabbaba karancin man na fetur.
A baya-bayan nan ne majalisar dattawan ta umarci mambobin kwamitin da su gudanar da binciken a dukkanin mazabun su, kan dalilan da suka sanya ake fuskantar karancin man fetur a halin yanzu, domin lalubo hanyoyin da za’a bi wajen dakile matsalar.
Ya kara da cewa ko da suka tambayi shugaban Kamfanin mai na kasa NNPc wato Maikanti Baru, ya shaida musu cewar sun ninka adadin man da suke fitarwa, sai dai duk da haka baya isar al’ummar kasar nan.
A cewar Kabiru Marafa abin takaici ne yanda al’ummar kasar nan ke daukar lokacin suna bin dogon layi, wajen siyan mai, kuma abin mamakin shine da dama daga cikin dillalan man fetur din na da hannu a karancin man na fetur da kasar nan take fuskanta.