Connect with us

Labarai

Majalisar dattijai ta amince da nadin Janar Faruk Yahaya a matsayin babban hafsan sojin Najeriya

Published

on

Majalisar dattijai ta amince da nadin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin babban hafsan sojin kasa na Najeriya.

Amincewar majalisar ya biyo bayan gabatar da rahoton hadin gwiwa da kwamitocin tsaro da na soji suka yi a yayin zaman majalisar na ranar Talata karkashin jagorancin Sanata Ali Ndume da Sanata Aliyu Wamakko.

Shugaban kwamitin tsaro na majalisar Sanata Aliyu Wamakko ne ya gabatar da rahoton.

Kafin tabbatar da shi, Janar Farouk Yahaya yana rike da mukamin ne a matsayin riko bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi sakamakon rasuwar Laftanar Janar Ibrahim Attahiru a wani hatsarin jirgin sama.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!