Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsaro: sojoji sun cafke dan bindiga – sojoji

Published

on

Rundunar sojin kasar nan ta ce dakarunta da ke sintiri a kan hanyar Mokwa zuwa gadar Jebba sun samu nasarar cafke wani ‘dan.

Sojojin sun cafke shi ne a cikin mota lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa garin Badin bayan ya baro garin Zuru na Jihar Kebbi.

Daraktan yada labaran rundunar Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya tabbatar da hakan.

Janar Nwachukwu ya ce sun gano shi ne a cikin mota lokacin da suke binciken fasinjoji, inda suka samu tarin kakin soja da takalman sojoji da wuka da kuma wasu kayan tsafe-tsafe a wurinsa, har ma ya yi karyar cewa shi soja ne kuma sunansa Saja Aminu Sule.

Daga bisani ya ce yana kan hanyar zuwa garin Ogbomosho ne da ke jihar Oyo, kuma kakin na ‘dan uwansa ne wanda soja ne.

Tuni dai an mika shi hannun ‘yan sanda na Mokwa don fadada bincike a kansa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!