Labarai
Majalisar dattijai ta bayyana matsayar ta kan batun ƙirƙiro sabbin jihohi
Majalisar dattijai ta ki amincewa da batun shawarar kirkirar sabbin jihohi.
Kwamitin majalisar kan gyaran kundin tsarin mulkin kasa na shekarar 1999 ya ce, bai yi shawarar kirkiro sabbin Jihohi 20 ba a yanzu.
A cewar kwamitin, an jawo hankalin sa kan wani rahoto da kafofin yada labarai ke yadawa cewa, kwamitin ya ba da shawarar ƙirƙirar ƙarin Jihohi 20 a Najeriya.
Kwamitin ya ce babban kuskure ne batun sake kirkiro jihohi, sai dai matukar akwai bukatar hakan to kuwa sai an bi wasu ƙa’idojin sashe na 8 na kundin tsarin Mulkin Najeriya na 1999 tare da yi masa kwaskwarima.
Cikin ƙa’idojin kuwa kwamitin ya ce, har da batun samun rinjaye da kaso biyu cikin uku na wakilan majalisar, kan batun ƙirƙirar sabbin jihohin.
You must be logged in to post a comment Login