Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan Tifa sun sake gina wata gada da ta lalace

Published

on

Kungiyar direbobin Tifar yashi ta jihar Kano reshen kwanar ‘yan Tifa ta gina wata katafariyar Gada a Karamar hukumar Nasarawa domin ragewa gwamnati nauyin dake kanta.

Shugaban Kungiyar Direbobin Tifar yashi ta kasa shiyar Kano Kwamared Mamuni Ibrahim Takai ne ya shaida hakan lokacin bikin bude katafariyar Gada da reshen Kwanar Tifa suka gina.

Mamuni Ibrahim Takai ya ce ‘yan kungiyar sun dauki matakin sake gina gadar ne bayan karyewa da ta yi domin su ragewa Gwamnati aiki da kuma taimakawa mazauna yankin baki daya.

Shugaban kungiyar Mamuni Takai ya kuma yi kira ga sauran mambobin kungiyar dasu rika gudanar da ayyukan alkairi a yankunan da suke gudanar da sana’ar domin farantawa al’ummar yankunan.

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito Shugaban Kungiyar reshen Kwanar Tifa Yahya Sadi Adamu na yabawa sauran mambobin kungiyar bisa kokarin da suka yi, inda kuma kara tabbartar da cewa za su ci gaba gudanar da ayyukan alkairi a unguwar.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!