Labarai
Majalisar dokoki ta buƙaci gwamnatin Abba Gida-gida ta gyara matatar ruwa ta Kafinciri
Majalisar dokokin Kano ta buƙaci gwamnatin Engr. Abba Kabir Yusuf, da ta gyara matatar ruwa ta Kafinciri domin inganta samar da ruwan sha a karamar hukumar Garko da kewaye.
Majalisar ta buƙaci hakan ne a zamanta na yau Talata biyo bayan ƙudurin da wakilin ƙaramar hukumar Garko a zaure Murtala Muhammad Kadage, ya yi.
Dan majalisar na Garko Murtala Muhammad ya ce, akwai Injina da ke buƙatar gyara a gidan ruwan sannan kuma da buƙatar inganta walwalar ma’aikata da kuma samar da tsaro a wurin.
A dai zaman na yau ƙarƙashin jagorancin Jibril Isma’il Falgore, Majalisar dokokin ta Kano, ta kuma buƙaci gwamnatin jiha ta gina titin da ya tashi daga Lajawa zuwa garin Dadin Kowa da ke iyaka da ƙaramar hukumar Ajingi.
Dan majalisa mai wakiltar Wudil Ali Abdullahi, ne ya gabatar da kudurin yana mai cewa samar da titin wanda ke da tsawon kilomita goma sha biyu zai taimaka wajen bunƙasa harkokin Noma a yankin.
You must be logged in to post a comment Login