Kaduna
Majalisar Dokokin Jahar Kaduna ta mayar da rahotanin kwamatocin majalisar biyu ga ‘yan kwamatin domin sake gyara akan su

Majalisar Dokokin Jahar Kaduna ta mayar da rahotanin kwamatocin majalisar biyu ga ‘yan kwamatin domin sake gyara akan su kafin a amince dasu.
Majalisar a zamanta na Talatar nan tun da fari ta bukaci Shugaban marasa rinjaye na majalisar Ali Kalat da ya gabatar da rahotan kwamatin sa kan kafa Hukumar koyar da sana’o’i ta Jahar wanda kudiri ne na Majalisar zartarwa.
Kazalika shima shugaban kwamatin Ilimi na majalisar Barista Muhamud Lawal Ismail ya gabatar da rahotan sa wanda dukaninsu aka mayar dasu ga kwamatocin domin sake gyare-gyare akan su, kamar yadda Barista Muhamud Lawal Ismail yayi ma wakilin mu karin haske kan yadda ta kasance a majalisar.
Majalisar dai ta baiwa kwamatocin yan kwanaki kadan na kammala gyaran domin su kuma sake dawowa da majalisar rahotanin.
You must be logged in to post a comment Login