Connect with us

Labarai

Wasu yan bindiga sun sace jami’an kula da lafiya a matakin farko a jihar Nassarwa

Published

on

‘Yan bindiga sun sace wasu jami’an hukumar kula da lafiya a matakin farko na jihar Nassarwa guda uku.

Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar ta Nassarwa Kennedy Idrisu wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce, ma’ikatan uku suna tafiya ne a cikin wata mota kirar Toyota Hilux lokacin da ‘yan bindigar suka far musu a kauyen Bugan-Gwari.

Ya kuma ce ma’iakatan uku sun bar garin Lafiya babban birnin jihar don zuwa garin Gadabuke da ke yankin karamar hukumar Toto.

Sai dai ya ce tuni ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro suka bazama don neman inda ‘yan bindigar suka boye su.

Da ya ke karin haske kan batun, shugaban hukumar kula da lafiya a matakin farko na jihar Nassarwa Muhammed Adiz ya tabbatar da faruwar lamarin yana kuma mai bayyana lamarin a matsayin abin takaici.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,747 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!