Connect with us

Manyan Labarai

Majalisar dokokin jihar Kano ta yadda da kara sarakunan yanka guda hudu

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano ta sahale ga gyaran dokar masarautu ta jihar Kano wadda ta amince da kafa sabbin Sarakunan yanka masu daraja ta daya a jihar ta Kano guda hudu.

Hakan ya biyo bayan amincewa da sakamakon rahoton da shugaban masu rinjaye na majalisar Baffa Babba Dan-Agundi ya karanta.

Bayan daukar tsawon lokaci ‘ya’yan majalisar na zaman sirri kan batun dawowar su ke da wuya suka amince da dokar.

Da ya ke Karin haske kan dokar shugaban masu rinjaye na majalisar Baffa Babba Dan-Agundi, ya ce, jikokin Sarki Dabo su za su ci gaba da sarautar masarautar Bichi haka zalika masu nadin sarautar Kano su zasu zabi Sarki a kasar Bichi.

Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Danbatta ya kalubalanci lamarin yana mai cewa ba a yi adalci wa arewacin Kano ba sakamakon cewa sarakuna uku daga cikin hudu sun fitone daga kudancin Kano.

Yayin da a bangare guda majalisar ta amincewa gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da ya nada mai shari’a Nura a matsayin babban jojin jihar Kano.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,926 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!