Manyan Labarai
Majalisar dokokin Kano ta sahale gyaran dokar fanshon gwamnoni da mataimakin da ta Shugabanin majalisa
Majalisar dokokin jihar Kano a yau Talata 7 ga watan Mayu 2019, ta sahale gyaran dokar fanshon gwamnoni da mataimakin su da kuma na Shugabanin majalisa da mataimakin su.
Hakan ya biyo bayan amincewa da sakamakon rahoton kudirin dokokin yayin zaman na yau.
Da ya ke zantawa da manema labarai bayan zaman majalisar, shugaban masu rinjaye na majalisar Baffa Babba Dan-Agundi cewa ya yi dokar fanshon Shugabannin majalisar da na mataimakin su wadanda ba sa rike da wani mukami ne kawai za su amfani.
A wani labarin kuma majalisar dokokin jihar Kano ta sha alwashin tabbatar da gyaran dokar masarautar ta jihar Kano wanda zai ba da dama wajen kirkiro sabbin sarakunan yanka masu daraja ta daya a jihar Kano.
Shugaban majalisar Kabiru Alhassan Rurum ne ya bayyana lokacin da ya ke jawabi ga dubban al’ummomin kanananan hukumomin Rano da Gaya da Karaye da kuma Bichi wadanda suka kai ziyarar nuna goyon bayan kan kudirin majalisar kan dokar kirkiro sabbin masarautu a jihar ta Kano.
jama’a da dama ne suka halarci da suka fito daga kananan hukumomin hudu suka kai ziyara majalisar da safiyar yau.