Labarai
Majalisar dokokin jihar Kano ta zargi hukumar Kwastam da nuna bangaranci wajen daukar ma’aikata a jihohin Kasar nan

Majalisar dokokin Jihar Kano tayi kira ga gwamnatin tarayya karkashin gwamnatin Kano da ta duba yadda aka ɗauki ma’aikatan kwatsam a ƙasar nan.
Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Kano, Lawan Husaini Dala ne ya gabatar da kudirin a zaman majalisar na yau Talata. Inda ya bayyana cewa hukumar ta Kwastam tayi watsi da hukumar rabon arziki da hukumomin gwamnati a Najeria wajen samar da daidaito a fannin daukar aiki.
Hussaini Dala yace akwai rashin adalci kan yadda aka ɗauki ma’aikatan duba da yadda jihohin kudancin ƙasar nan suka mamaye kaso mafi tsoka daga ciki.
Wannan kudirin da Shugaban masu rinjaye na majalisar ya gabatar, ya samu goyon bayan mataimakin majalisar, Bello Ɓutu-ɓutu da na Doguwa, Salisu Ibrahim.
You must be logged in to post a comment Login