Kaduna
Majalisar Dokokin Kaduna ta amince da ƙudurin kula da ayyukan ’yan Gwangwan

Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da ƙudurin kula da ayyukan ’yan gwangwan a faɗin jihar, domin kare muhalli da hana lalacewar kadarorin gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu.
Dan Majalisa mai wakiltar Zaria Mahmud Lawal, ne ya bayyana hakan ga manema labarai.
Ya ce, akwai bukatar gyaran dokar Hukumar Kula da Muhalli ta Jihar Kaduna KEPA domin ta haɗa da kula da ayyukan ’yan gwangwan.
Majalisar ta ce, wannan mataki zai taimaka wajen tsaftace muhalli da kuma hana barna da lalata kayayyakin gwamnati da ake alakanta wa da wasu daga cikin ’yan gwangwan.
You must be logged in to post a comment Login