Labarai
Majalisar dokokin kano ta ƙara adadin kuɗin kasafin 2025 zuwa Biliyan 719
Majalisar dokokin jihar Kano ta ƙara adadin kuɗin kasafin shekarar 2025 daga biliyan 549 zuwa biliyan 719, wanda hakan ya biyo bayan buƙatu da koke-koken al’umma da suke yi, da kuma wasu sassa da gwamnatin bata mayar da hankali akan su ba
Shugaban masu rinjaye na majalisar Lawan Hussaini Dala ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan amincewa da kasafin shekarar 2025 da majalisar dokokin jihar tayi yau inda ya zama doka domin ya fara aiki a gobe 1 ga watan Janairun 2025.
Lawan Hussaini Dala ya ƙara da cewa wannan kasafin da aka amince da shi a yau ya zama doka haka kuma bangaren ayyuka yafi Kowane ɓangare samun babban kaso.
A dai zaman majalisar na yau dai ta amince da canja sunan jami’ar Yusuf Maitama sule zuwa ainayin sunan ta na farko wato Northwest.
Da yake jawabi ga manema labarai shugaban masu rinjaye na majalisar Lawan Hussaini Dala ya ce wannan canja sunan ya biyo bayan ƙudirin da aka samar da makarantar domin kuwa sunan ta na Northwest akwai manufar samar da shi.
Haka zalika yayin zaman majalisar tace zata tabbatar da duk mai yuwuwa domin ciyar da kano gaba.
You must be logged in to post a comment Login