Labarai
Majalisar Dokokin Kano Ta Amince Da Ibrahim Yakubu Adamu a matsayin kwamishina

Majalisar dokokin jihar Kano ta tantance shugaban hukumar tsara birane na jihar Arc. Ibrahim Yakubu Adamu da za’a naɗa a matsayin kwamishina kuma mamba a majalisar zartarwa ta jiha.
Arc Ibrahim Yakubu Adamu da za’a na naɗa a matsayin sabon kwamishinan yace zai ɗora akan irin ayyukan da ya saba yi a hukumar tsara birane ta jihar kano a duk inda ya tsinci kan sa domin bayar da ci gaba a faɗin jihar Kano.
Da yake amsa tambayoyi daga ƴan majalisun Arc. Ibrahim Yakubu ya jaddada mahimmancin sabunta ƙudiri na ci gaba da tsare-tsare na birane da yankunan karkara.
Ya kuma bayyana farin cikinsa da yadda Majalisar ta amince da shi, inda ya yi alƙawarin bayar da gudunmowarsa wajen sauke duk wani nauyi da aka ɗora masa a wannan lokacin.
Da yake jawabi Kakakin majalisar dokokin Kano Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore, ya buƙaci wanda aka zaɓa ya ci gaba da aiki tukuru, kamar yadda ya yi aiki tukuru a hukumar tsara birane ta jihar wato KNUPDA.
You must be logged in to post a comment Login