Labarai
Majalisar dokokin Kano ta buƙaci a gaggauta samar da ƙarin hanyar ratse ga masu ababen hawa a titin Hotoro
Majalisar dokokin jihar Kano ta buƙaci gwamnatin jihar Kano ta da yi gaggawar samar da ƙarin hanyar ratse ga masu ababen hawa.
An buƙaci samar da gadar ne wadda masu ababen hawa za su riƙa bi sakamakon aikin samar da titin ƙarƙashin ƙasa da gadar sama a shataletalen gidan mai na NNPC da ke hotoro a nan Kano.
Buƙatar dai ta biyo bayan ƙudurin gaggwa da ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Bebeji Abubakar Uba Galadima ya gabatar a zaman majalisar na Litinin ɗin nan.
Ɗan majalisar na Bebeji ya ce, “Tun bayan fara aikin mutane da dama da ke bin hanyar suka shiga cikin halin damuwa kasancewar an rufe hanyar kuma ga shi ta haɗa ƙananan hukumomin jihar Kano da dama ba ya ga sauran jihohin hanyar ke da su”.
Haka kuma Abubakar Uba Galadima ya ƙara da cewa, “Akwai wata hanyar ratse da ake amfani da ita daga gidan man Chula da ke kan titin Ring Road zuwa gidan mai Allo ta ɓulla garin Mariri, sai dai hanyar a buƙatar faɗaɗawa kasancewar ababen hawan da suka lalace na haifar da cunkoso”.
Bayan gabatar da ƙudurin ne sai shugaban majalisar Engr Hamisu Ibrahim Chidari, ya miƙa buƙatar kwamishinan ayyuka na jihar Kano da ya kai ziyara wurin aikin tare da ɗaukar matakan da suka dace.
Ƙudurin ya samu sahalewar ɗaukacin mambobin majalisar, inda har ma wasu daga ciki da suka haɗar da mataimakin shugaban majalisar Alhaji Zubairu Hamza Massu mai wakiltar Ƙaramar hukumar Sumaila da sauran wasu daga cikin ƴan majalisar suka bada gudunmawarsu yayin neman sahele ƙudurin.
You must be logged in to post a comment Login