Labarai
Majalisar dokokin Kano ta buƙaci Ƴan sanda da gwamnati su yi gaggawar magance hare-haren ƴan Daba
Majalisar dokokin Kano, ta buƙaci Kwamishinan ƴan sanda da gwamnatin jihar da su yi gaggawar samar da tsaro ga sassan da ayyukan ƴan daba ke ci gaba da ƙamari a ƴan kwanakin nan.
Buƙatar dai ta biyo bayan ƙudurin gaggawa da ɗan majalisar mai wakiltar ƙaramar hukumar Dala kuma shugaban masu rinjaye Alhaji Lawan Husaini Cheɗiyar ƴan Gurasa, ya gabatar yayin zaman majalisar na yau Litinin.
Da yake gabatar da ƙudurin, ɗan majalisar na Dala, ya ce a baya-bayan nan al’ummar sassan ƙaramar hukumar da ya ke wakilta ba sa iya yin bacci sakamakon harin ƴan daba.
Haka kuma ya ƙara da cewa, yanzu haka kusan kwanaki bakwai kenan mazauna yankunan Dala da Dogon Nama da Madigawa da Rijiya Biyu da Sanka da sauransu suna fama da matsalar harin ƴan Daba da ke fasa motoci da shagunan mutane har ma da cinna wuta a kan dukiyar al’umm.
Da yake goyon bayan ƙudurin, ɗan majalisa mai wakiltar Rimingado da Tofa kuma mataimakin shugaban majalisar Muhammad Bello Butu-Butu, ya ce, yanzu haka a sassan jihar Kano akwai unguwanni da dama da suke fuskantar irin wannan matsala don haka ya kamata a gaggauta ɗaukar wannan mataki.
You must be logged in to post a comment Login