Labarai
Majalisar dokokin Kano ta bukaci gwamnati ta gaggauta daukar matakan tsaro a wasu yankuna sakamakon matsin lambar yan ta’adda.

Majalisar dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar da ta dauki matakin gaggawa kan matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara a Tsanyawa da Bagwai.
Wannan kiran ya biyo bayan kudiri na gaggawa da ‘yan majalisar da ke wakiltar yankunan suka gabatar yayin zaman da kakakin majalisar Jibril Isma’il Falgore ya jagoranta.
Masu gabatar da kudirin, Ali Lawan Alhassan Kiyawa da Garba Ya’u Gwarmai, sun ce matsalolin satar shanu, garkuwa da mutane da kisa sun ƙaru sosai a ‘yan kwanakin nan.
Majalisar ta bukaci gwamnati ta ƙara jami’an tsaro da kuma fitar da kuɗaɗen tallafi ga hukumomin da abin ya shafa, don kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
You must be logged in to post a comment Login