Labarai
Majalisar Dokokin Kano ta bukaci gwamnati ta gyara hanyoyi a Kura da Garun Malam da Rano

Majalisar dokokin Kano ta bukaci gwamnatin jihar ta gaggauta kai wa al’ummar yankunan Garun Malam zuwa yada kwari da Titin zuwa Zaria dauki wajen gyara hanyarsu da tsayinta ya haura fiye da kilomita 30.
Dan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Kura da Garun Malam Zakariyya Alhassan, ne ya bayyana hakan a zaman majalisar na yau Talata domin ɗaukar matakin gaggawa wajen magance matsalart da ga al’ummar yankin ke fuskanta.
A dai zaman majalisar na yau Ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Rano Hon Ibrahim Malami Rano shi ma ya gabatar da ƙudirin gaggawa ga inda ya yi kira ga gwamnatin kano da a gyara hanyar tsohuwar kasuwa ta ƴan Barkono zuwa Gwangwan ta shiga Gobura ta hada da garin Saji.
Majalisar Dokokin ta jihar Kano, ta kuma sha alwashin ganin ta tura buƙatun ga gwamnati domin ɗaukar matakin gyara a kan lokaci.
You must be logged in to post a comment Login