Labarai
Majalisar dokokin Kano ta duba yadda aikin gina sansanin Kano Pillars ke gudana

Majalisar dokokin jihar Kano, ta yaba da yadda ake gudanar da aikin gina sansanin ƴan wasan ƙungiuar Kano Pillars da ake gina wa a tsohuwar tashar mota da ke New Road a unguwar Sabon Gari.
Shugaban Kwamitin hakokin wasanni na Majalisar, Kabiru Dahiru Sule, ne ya yaba da yadda aikin ke gudana yayin wani rangadin duba ayyuka da suka kai wurin tare da sauran mambobin kwamitin.
Ya ce aikin ya na tafiya cikin gamsarwa, kuma ci gaban da ake samu ya karu matuka.
Yayin rangadin duba aikin, Kabiru Dahiru ya samu rakiyar ƴan majalisar da dama da suka haɗar da shugaban masu rinjaye na zauren Lawan Husaini da Aliyu Yusuf Daneji na karamar hukumar Birni da Ibrahim Muhammad na Rano da kuma Usman Abubakar Tasi’u na Kiru sai Ayuba Labaran Durum na Kabo.
You must be logged in to post a comment Login