Connect with us

Labaran Kano

Majalisar dokokin Kano ta katse hutun da take yi , zata dawo aiki gobe

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano ta katse hutun da saba  yi a yanzu, inda za ta dawo gobe Laraba ashirin da bakwai ga watan Nuwamba  domin ci gaba da zama kamar yadda ta sabayi.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da akawun majalisar dokokin ta Kano Abdullahi Alfa ya fitar mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai na majalisar Ali Bala Kofar Kudu.

Sanarwar ta ce majalisar ta katse hutun da ta ke yi ne wanda a baya aka tsara cewar za ta dawo domin ci gaba da zama a ranar goma sha shida ga watan gobe na Disamba domin kammala ayyukan da ke gabanta.

Sai dai sanarwar ba ta yi karin haske kan dalilai  da Kuma ayyukan da suka sa majalisar ta katse hutun da ta ke yi ba domin fara zama a gobe Laraba.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!