Connect with us

Manyan Labarai

Gwamnatin tarayya za ta rage jinkiri a shari’u-  Buhari

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari  yayi kira ga alkalai kan samar da wasu kotuna dan samun sauki wajan gudanar da sharia

Shugaban yayi wannan nan jawabi ne a lokacin da yake ganawa da manyan alkalai na kasa  a garin Abuja.

Shugaba Muhammadu Buhari ya fara da bawa kungiyar alkalai ta kasa shawara wajan  samar da isassun Kotuna na musamman  domin samun sauki wajan gudanar da shari’u  da rage yawan cinkoso wajan shari’a .

A wata  sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar daga mai bashi shawara akan kafafen yada labarai Mr Femi Adesina yace shugaban yace manyan jami’an harkokin shari’a suna fuskantar matsaloli kuma  sun tattauna da babban jojin kasa Ibrahim Tanko Muhammad.

Shugaban ya kara da cewa Gwamnati ta jajirce kan tabbatar da sauye sauye wajan canja wasu dokoki da  suke da tsauri da kuma samar da sababbi domin inganta rayuwar ‘‘yan Najeriya.

Bayan haka shugaban yace suna aiki kud da kud da babban jojin kasa wajan tabbatar da kasafin kudin da aka warewa bangaran sharia ya karu domin tabbatar da yayi daidai da bukatun su.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!