Labarai
Majalisar dokokin Kano ta nemi a haramtawa kwastam aiki a cikin gari.
Majalisar dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jiha da ta bukaci hukumar yaki da fasakwauri ta kasa kwastam da ta gudanar da bincike tare da hukunta jami’anta da ake zargi suna da hannu a harbin wani mutum wanda hakan ya janyo sanadiyyar rasuwarsa a kan titin zuwa Hadejia.
Bukatar ta biyo bayan kudurin gaggawa da dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Gezawa Alhaji Isyaku Ali Danja ya gabatar a zaman majalisar a ranar Laraba 03 ga watan Maris.
Da yake gabatar da kudurin, Alhaji Isyaku Ali Danja, ya ce, wasu jami’an hukumar yaki da fasakwauri da ke kan hanyar ne suka biyo mtumin wanda mazaunin cikin garin Kano ne amma yana ziyartar danginsa a karamar hukumar Gezawa inda suka harbe shi har ta kai motarsa ta yi hatsari ya rasa ransa.
Haka kuma ya ce, binciken da aka yi yayin hatsarin na sa ya nuna cewa babu komai a cikin motarsa wadda jami’an hukumar ke zaton cewa ya debo kayan fasakwauri ne a cikinta.
‘‘Kamata ya yi majalisar ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin an biya iyalansa diyya kasancewar an hallaka shi ne bisa ganganci’’.
‘‘Haka zalika wajibi ne a haramtawa jami’an hukumar gudanar da aiki a cikin gari wanda ake zarginsu da biyo masu ababen hawa a cikin gari a guje wanda hakan kuwa ya saba da ka’idar aikinsu’’ a cewar Ali Isyaku Danja.
Bayan kammala gabatar da kudurin ne, mambobin majalisar da suka hadar da mataimakin shugaban majalisar Zubairu Hamza Massu, da tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar Alhaji Kabiru Hassan Dashi da mamba mai wakiltar karamar hukumar Ungogo Aminu Sa’adu suka goyi bayan kudurin tare dayin karin bayani kan irin hallaka mutanen da jami’an na Kwastam ke yi.
You must be logged in to post a comment Login