Labarai
Majalisar dokokin Kano ta raba kayan aiki ga kwamitocinta
A ƙoƙarin ganin an ƙara inganta ayyukan Majalisar dokokin jihar Kano musamman na sanya ido da bibiya na ƴan Majalisa da sauran hukumomin watau Oversight Function, Shugaban Majalisar Alhaji jibril Ismail Falgore, ya bayar da umarnin samar da isassun kayan aiki ga sakatarorin kwamitoci 34 na majalisar domn ci gaba da gudanar da ayyukan kwamitocin yadda ya kamata.
Shugaban majalisar ya bayar da umarnin ne yayin da ya ke bai wa wasu daga cikin sakatarorin kwamitocin kwamfutoci samfurin Laptop.
Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban majalisar kuma sakataren yaɗa labaran majalisar Kamaluddeen Sani Shawai ya fitar.
Sanarwar ta ce, Da ya ke yin ƙarin haske kan batun, Shugaban ma’aikatan hukumar gudanar Majalisar Alhaji Bashir Diso, kira ya yi ga bukaci ma’aikatan da su kara ƙaimi wajen inganta ayyukansu.
Haka kuma sanarwar ta ruwaito cewa, cikin kayayyakin da aka bai wa sakatarorin kwamitocin sun hada Kwamfutocin Laptop da sauran kayan aiki gami da samar da horo musamman kan harkokin gudanarwar aiki.
You must be logged in to post a comment Login