Labarai
Majalisar dokokin kano ta yi dokar tarar dubu 25 ga duk wanda aka kama da tofar da yawu da majina akan tituna

Majalisar dokokin Kano ta yi dokar cin tarar naira dubu 25 ga duk wanda aka kama da tofar da yawu, majina, yin bahaya ko zubar da Shara a sha tale-tale da karkashin gadojin dake Kano.
Wannan ya biyo bayan dokar da majalisar ta Samar wadda zata gudanar da ayyukan hukumar kawata birnin Kano da Kula da wuraren shakatawa.
Da yake Karin bayani ga manema labarai, Shugaban masu rinjaye na majalisarLawan Hussaini Dala yace, ya zama wajibi gwamnati ta dauki matakan da zasu tsaftace Kano domin shigar da jihar sahun biranen duniya a fannin tsafta da cigaba.
Lawan Hussaini Dala yace, bayan tarar ta naira dubu 25, akwai Kuma sauran hukunce-hukunce da dokar ta tanada wadanda za’ayi amfani dasu wajen ladabtar da duk wanda aka samu da laifukan
Majalisar ta kuma yi karatu na biyu kan gyaran dokar hukumar kwashe Shara da tsaftar Muhalli ta Kano domin Samar da mataimakin Shugaba.
You must be logged in to post a comment Login