Labarai
Majalisar dokokin zasu kafa kwamitin da zai yi kan kutse majalisar dattija
Majalisun dokokin kasar nan za su kafa kwamiti da zai binciki dalilin da ya sanya wasu tsageru suka yi kutse cikin zauran majalisar dattijai suka kuma sa ce sandar majalisar a ranar Larabar da ta gabata.
Shugaban majalisar dattijai Abubakar Bukola Saraki ne ya sanar da hakan jim kadan bayan kammala wani dogon zaman sirri da majalisun suka gudanar a jiya.
A don hakan ne Saraki ya bukaci al’umma da su yi hakuri da matakin da majalisar za ta dauka na kara karfafa tsaro a harabar majalisar ta dattijai.
Ya kuma sanar da cewa kwamitin hadakar zauran majalisun zai yi bincike dalla-dalla kan yadda al’amarin ya faru domin kamo masu laifin da hukunta su.
A cewar Saraki, an dorawa kwatan da zai yi binciken da ya tsananta bincike akan shugaban hukumar tsaro ta DSS Lawan Daura da kuma babban sifeton yan sandan kasar nan Ibrahim Idris.
Cikin abinda kwamitin zai nazar ta har da yadda za a kare ginin majalisar daga shigar kowa da kowa ta yadda za a kara t