Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majalisar Kano ta amince da nadin karin wasu kwamiahinoni uku

Published

on

Majalisar dokoki a jihar Kano, ta amince wa gwamna Engr. Abba Kabir Yusuf, damar ƙara naɗa sababbin Kwamishinoni uku.

Amincewar na zuwa ne a Wani zama na musamman da majalisar ta gudanar a yau Alhamis bayan da shugaban majalisar Jibril Isma’il Falgore ya karanta wasiƙar da gwamna ya aike mata domin neman sahalewar.

Bayan karanta wasiƙar ne ɗaukacin mambobin majalisar suka amince da karawar mutanen, tare da umartarsu da su halarci zaure majalisar da misalin ƙarfe 1:00 na ranar yau Alhamis domin tantance ce su.

Sababbin kwamishinonin sun haɗa da: Alhaji Ibrahim Jibrin daga ƙaramar hukumar Fagge, sai Ibrahim Ali Namadi daga Dala, da kuma Hajiya Amina Abdullahi daga ƙaramar hukumar Nassarawa.

Freedom Radio ta ruwaito cewa a zaman na yau, shugaban majalisar ya kuma karanta wasiƙar da gwamnan ya buƙata na a tantance Mai shari’a Dije Abdu Aboki domin naɗa ta a matsayin babbar jojin a jihar Kano.

Rahoton: Auwal Hassan Fagge

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!