Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majalisar Kano ta sanya ranar tantance sabbin Kwamishinoni

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano ta sanya ranar 2 ga watan gobe na Afrilu domin tantance wadanda gwamnan ya tura sunayensu domin naɗa su a matsayin Kwamishinoni kuma wakilai a majalisar zartaswar jiha.

Majalisar ta bayyana hakan ne a zamanta na yau Talata bayan da ta karbir wasikar bukatar hakan daga Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf.

Ta cikin wasikar, gwamnan ya aika wa majalisar sunayen mutane 4 da ya bukaci ta tantance su tare da nada su a matsayin kwamishinoni kuma wakilai a majalisar zartaswa.

Mutanen da gwamnan ya tura da sunansu sun hada da Adamu Aliyu Kibiya da Usman Shehu Aliyu da Abduljabbar Umar Garko da kuma Babban dan tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso watau Mustapha Rabi’u Musa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!