Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buɗe Iyakar Nijeriya barazana ce ga sana’armu: RIFAN

Published

on

Kungiyar masu sarrafa shinkafa ta Nijeriya, wato RIFAN, ta bayyana damuwa game da matakin gwamnatin kasar na dage haramcin shigar da wasu kayayyaki daga kasashen waje ciki har da shinkafa.

 

Shinkafa na cikin kayayyakin da gwamnatin Najeriya ta haramta shigar da su a shekarar 2015 cikin kasar a wani mataki na kokarin bunkasa noma a kasar da nufin dogaro da kai.

 

Kungiyar masu sarrafa shinkafar ta cikin gida, ta ce matakin dage haramcin babbar barazana ce bayan sun zuba makudan kudi a kasuwancin.

 

Shugaban kungiyar, Peter Dama, ya shaida wa BBC cewa, a gaskiya wannan mataki ya zame musu kamar bala’i ne domin gwamnati ta sanya sun sanya kudadensu sun sayi kayan sarrafa shinkafa, sannan an sa jama’a sun shiga noma shinkafar, ga shi jama’ar kasa sun fara son shinkafar da ake samarwa a gida, “sai kawai mu ji an ce an dage haramcin shigo da shinkafar waje.”

 

Ya ce, ” Wannan mataki na gwamnati ya kawo mana cikas, ga shi kuma zai sa a rufe kamfanoni da dama, sannan jama’a da yawa za su rasa aikin yi ga shi kuma manoma da dama kuma ba za su yi aikin shinkafa, kuma sannan za a tara shigo mana da shinkafar da ta riga ta rube.”

 

Peter Dama, ya ce: “Gwamnati ba ta shawarce mu ba kafin ta dauki wannan mataki, kuma batun cewa shinkafar da ake samarwa a gida ma tana tsada ai kowa ya san ba da ruwa ake nomata ba, kuma yadda ake noman nata ma ai sai a duba a gani, sannan wajen ban ruwa ba wasu da kananan inji suke yi kuma ai da man fetur ake amfani a injin, kuma kowa ya san tsadar mai a yanzu.”

 

Shugaban ya ce babbar damuwarsu idan har aka fara shigar da shinkafar waje to mutane sai su koma kanta domin su al’ummar Najeriya idan aka ce musu ga wani abu na waje ko da ruwan sha ne sai hankalinsu ya koma kansa.

 

Ya ce, ” Mu mun yi iya bakin kokarin mu wajen nunawa yan Najeriya cewa shinkafarmu ta gida ta fi afki sannan ta fi amfani a jiki domin mu ta mu ba a ajiye ta ta yi shekara da shekaru ba.”

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!