Labarai
Majalisar Wakilai na shirin yin gyara ga dokar zaɓe

Majalisar Wakilan Najeriya, ta gabatar da sabon shirin da zai mayar da zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnonin jihohi zuwa watan Nuwamban shekarar 2026.
Wannan gyara na cikin dokokin da ake son sabuntawa domin a rage jinkirin shari’un zaɓe kafin a rantsar da sabbin shugabanni a ranar 29 ga Mayun shekarar 2027.
Shugaban kwamitin Majalisar Wakilai kan harkokin zaɓe, Adebayo Balogun, ne ya bayyana haka ya na mai cewa shirin zai tabbatar da cewa an kammala dukkan shari’un zaɓe kafin rantsuwar sabbin shugabanni.
Ya kuma ce, sabon tsarin ya tanadi rage lokacin da ake dauka wajen shari’a, tare da bai wa jami’an tsaro da ma’aikatan hukumar INEC, da ‘yan jarida damar yin zaɓe tun kafin ranar gudanar da zaɓe a faɗin ƙasa.
Haka kuma, an tanadi hukunci ga jami’an da ba su cika sharuddan dokar ba, ciki har da tara ko ɗaurin gidan yari.
INEC da wasu ƙungiyoyi masu ruwa da tsaki sun nuna goyon bayansu ga wannan shirin, musamman batun isar da sakamakon zaɓe ta hanyar anfani da fasahar zamani.
Sun bayyana cewa hakan zai taimaka wajen tabbatar da gaskiya da ingancin zaɓe da kuma rage yawan rikice-rikicen bayan zaɓe a faɗin Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login