Labarai
Majalisar Wakilai ta nemi goyon bayan Aminu Dantata
Majalisar wakilan Nijeriya, ta buƙaci haɗin kan ƴan ƙasar da su mara mata baya a ƙoƙarinta na ganin an sauya tsakin mulkin ƙasar nan daga na shugaban ƙasa mai cikakken iko zuwa na shugaban ƙasa da Fira minista.
Shugaban marasa rinjaye na majalisar Kingsley Chinda ɗan majalisa daga jihar Rivers, ne ya buƙaci hakan yau Alhamis lokacin da suka ziyarci Alhaji Aminu Alhassan Dantata a gidansa da ke nan Kano.
Da yake jawabi, shugaban tawagar, Kingsley Chinda, ya bayyana cewa, kimanin mambobin majalisar 60 ne suka haɗa kai wajen gudanar da kudurori uku na ganin an sauya tsakin shugabancin ƙasar nan, wanda suke da yaƙinin zai sauƙaƙa halin da ƙasar nan ke ciki.
“Mambobi 59 da kuma Ni na cikon 60 ne muka gabatar da ƙuɗurori har guda 3 kan wannan sauyi, kuma muna da yaƙin in cewa zai haifar da Ɗa mai ido.”
“Muna roƙon ku ƴan jarida da ku faɗakar da mutane irin muhimmanci da kuma alfanun wannan ƙuduri kuma su mara masa baya”, Inji shi.
A wannan tsari Ƴan majalisa ne za su zaɓi shugaban ƙasa a cikinsu, haka ma gwamnoni da sauran shugabani, kuma ƴan majalisa su ne Ministoci, don haka duk abinda za a gudanar dama kowa ya san shi saboda dama da shi aka tsara”, cewar Kingsley Chinda.
A nasa ɓangaren, Dattijon ƙasa Alhaji Aminu Alhassan Dantata, ya bayyana farin cikinsa bisa ƴunƙurin ƴan majalisar ya na mai cewa, yin sauyin ya dace, don kuwa zai taimaka musamman ya fuskar magance matsalolin da ƴan Nijeriya ke fuskanta.
“A yanzu haka ana sayar da Dalar Amurka a kan fiye da Naira 1,500, wannan babbar matsala ce da ya kamata a gyara, sauya wannan tsarin mulki zai taimaka matuƙa musamman wajen rage yawan kashe kuɗaɗen gwamnati.” Inji Dantata.
Alhaji Aminu Alhassan Dantata, ya kuma yi wa ƙasar nan addu’ar samun sauyi da zai sauƙaƙa irin halin matsin da al’umma ke fama da shi.
You must be logged in to post a comment Login