Kasuwanci
Majalisar Wakilai ta yi wa dokar hukumar Bincike da ci gaban albarkatun ƙasa kwaskwarima

Majalisar Wakilai, ta amince da dokar gyaran hukumar Bincike da ci gaban albarkatun ƙasa watau Raw Materials Research and Development Council, wadda ta tanadi cewa dole ne a ƙara darajar akalla kashi 30 cikin 100 ga kayan albarkatun ƙasa kafin a fitar da su zuwa ƙasashen waje.
Manufar wannan doka ita ce ƙarfafa masana’antun cikin gida domin a daina fitar da kayan albarkatun ƙasa kai tsaye ba tare da sarrafawa ba, tare da samar da ƙarin ayyukan yi da kuma inganta tattalin arzikin ƙasa.
Masana sun bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wajen farfaɗo da masana’antun sarrafa kayan albarkatu da kuma ƙara wa Najeriya samun kuɗaɗen shiga daga kayayyakin da take fitarwa zuwa waje.
You must be logged in to post a comment Login