Labarai
Majalisar zartaswa ta amince da ware fiye da biliyan 209 wajen aikin tituna
Majalisar zartaswa ta kasa ta amince da ware sama da naira biliyan 209 wajen cigaba da aikin gina titunan Kano zuwa Katsina da kuma wanda ya tashi daga Ibadan zuwa Ilesha ya bi ya ta Ife.
Ministan ayyuka da gidaje Babatunde Fashola ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai, bayan kammala taron majalisar zartaswa ta kasa karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.
Babatunde Fashola ya ce, kaso na biyu na aikin titin Kano Katsina zuwa Katsina wanda ya fara daga Gidan Mutum Daya zuwa kamfanin mulmula karafa na Katsina an ware masa naira biliyan 29 da miliyan 600.
Sai kuma aikin titin Ibadan zuwa Ilesha ya bi ya ta Ife an ware masa naira biliyan 79 da miliyan 800.
Ministan ya kuma ce an ware sama da naira biliyan 200, domin ci gaba da ayyukan tituna da suka hade da gadar Niger ya hada biranen Onitsha da Asaba.