Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majilisar dokokin kano ta amince da mutane 7 da gwamna ya turo mata a matsayin Kwamishinoni

Published

on

Majalisar dokokin Kano tace ta amince da mutane bakwai da gwamna Abba Kabir Yusif ya aike domin tantancewa ya naɗa su a matsayin kwamishinoni Kuma ƴan majalisar zartarwar jihar nan.

Shugaban masu rinjaye na majalisar Lawan Hussaini Dala ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala tantance mutanen bakwai.

A cewar Dala dukkanin waɗanda gwamnan ya turo majalisar nagartattu ne Kuma masu kishi da San cigaban Kano

Dala ya Kara da cewar tantancewar tasu ta mayar hankali ne bangaren da kowanne su yake da kwarewa.

Haka zalika majalisar tace a yau zata aikewa gwamna Abba da rahoton ta domin bashi damar rantsar da su da Kuma tura su ma’aikatun da zasu yi aiki.

Cikin kwamishinonin sun haɗar da.

1. Shehu Wada Sagagi
2. Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya
3. Dr. Isma’il Ɗan Maraya
4. Ɗahiru Muhammad Hashim
5. Engr. Gaddafi Sani Shehu
6. Comrade Abdulkadir Abdussalam.
7. Nura Iro Ma’aji

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!