Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Makaman da muke da su, sun tsufa – Babban hafsan tsaron Najeriya.

Published

on

Babban hafsan tsaron ƙasar nan Janar Lucky Irabor, ya ce, sojojin Najeriya ba za su iya samun nasarar kakkaɓe ayyukan ƴan ta’adda ba, matukar ba a samar musu da makamai na zamani ba.

 

A cewar sa, dalilin hakan ne ya sanya sojojin ƙasar nan su ke ƙokarin sayo sabbin makamai don yaƙi da ƴan ta’adda.

 

Janar Lucky Irabor ya bayyana hakan ne a wajen taron cin abici da aka shirya don karrama sojojin da suka kammala karatu a kwalejin manyan hafsoshin soji da ke Jaji a jihar Kaduna.

 

Babban hafsan sojin na Najeriya, ya kuma ce, samun nasara kan ƴan boko haram da sauran ƴan ta’adda da ke aikata ta’asa a sassa daban-daban na ƙasar nan, yana buƙatar ɓullo da sabbin dabaru waɗanda za su taimaka wajen kawo ƙarshen matsalara baki  ɗaya maimakon dogara ga soji kawai.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!