Connect with us

Ƙetare

Makwabtan Iran na fargabar illar hare-haren Amurka da Isra’ila

Published

on

Makwabtan ƙasar Iran na nuna matuƙar damuwa kan yiwuwar rikici ya bazu a yankin, bayan hare-haren da  Amurka da Israel suka kai.

 

Rahotanni sun ce ƙasashen Gulf da ke bai wa Amurka masaukin sojoji na tsoron Iran ta kai harin ramuwar gayya kan sansanonin sojin Amurka ko muhimman cibiyoyin more rayuwa kamar tashoshin wutar lantarki da matatun ruwa.

 

A baya, Iran ta kai hari kan sansanin sojin Amurka na Al-Udeid da ke Qatar bayan harin da aka kai kan cibiyoyinta na nukiliya.

 

Masu sharhi na ganin idan aka samu sauyin gwamnati da karfi daga waje, Iran na iya fadawa cikin rikicin cikin gida kamar yadda ya faru a Libya bayan kifar da Muammar Gaddafi.

 

Haka kuma, ƙasashe kamar Turkey na fargabar ƙungiyoyin Kurdawa za su yi amfani da rikicin, musamman masu alaƙa da PKK.

 

Pakistan na iya fuskantar matsalar tsaro idan rikicin ya ketare iyaka. Haka kuma ƙungiyoyin da Iran ke mara wa baya kamar Houthis a Yemen da Hezbollah a Lebanon na iya shiga lamarin.

 

Masana sun yi gargadin cewa rikicin na iya haifar da kwararar ‘yan gudun hijira kamar yadda ya faru bayan yaƙin basasar Syria a 2015. Ƙasashe kamar Turkey, Azerbaijan da Armenia na cikin masu nuna damuwa.

 

Hare-haren na iya janyo rufe mashigin Strait of Hormuz, inda kusan kashi 20% na man fetur na duniya ke bi ta nan. Wannan na iya jefa ƙasashen Gulf cikin matsalar kuɗi, tare da tasiri ga kasuwannin duniya, musamman ga China wadda ita ce babbar mai shigo da mai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!