Connect with us

Labarai

Malam Ibrahim Khalil ya zama shugaban malaman Arewa maso yamma

Published

on

Gamayyar malaman addinin musulunci sun zaɓi Malam Ibrahim Khalil a matsayin shugaban majalisar malamai shiyyar Arewa maso yamma.

Zaɓen na sa ya biyo bayan taron da gamayyar malaman yankin suka gudanar a birnin Katsina aranakun Jumu’a da Asabar 16 da 17 ga watan Oktoban da muke ciki.

Kafin wannan zaɓe dai, Sheikh Ibrahim Khalil shi ne shugaban majalisar malamai ta ƙasa reshen jihar Kano.

A yayin taron an kuma zaɓi shugaban majalisar malamai na jihar Jigawa Khadi Bashir Umar Birnin Kudu a matsayin babban sakataren majalisar malaman na yankin Arewa maso yamma.

Tuni majalisar malamai ta Kano ta aike da saƙon taya murna ga waɗanda aka zaɓa ta bakin sakataren majalisar Malam Ibrahim Tofa, yana mai an yi zaɓen bisa cancanta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,104 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!