Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Malaman addini dasu ake damawa a bangaren siyasa a manyan kasashen duniya-Dr Ibrahim Ilyasu

Published

on

  • A kasashen da suka ci gaba malaman addini nada rawar takawa a fannin siyasar kasashen.
  • Dr Ibrahim Ilyasu ya ce “akwai gyare-gyare da dama Daya kamata ayiwa bangaren siyasar kasar.
  • ya kamata suma mutane su daina siyasar akida.
  • tare da fayyace mutane ire-iren mutane daya kamat su zaba a matsayi wadanda zasu mulke su.

Wani malamin addinin musulunci a Jihar Kano ya bayyana cewa malaman addini ne ke juya akalar siyasa a kasashen da suka cigaba, sabanin Nijeriya.

Limamin masallacin Ubaiyi Bn Ka’ab dake Unguwar gama a karamar hukumar Ungoggo ” ne ya bayyana hakan yayin taron da cibiyar samar da zaman lafiya ta Islamic centre for peace building reshen Jihar Kano ta shirya kan gudunwar malamai wajen samar da zaman lafiya a lokacin gudanar da zaben dake tafe.

Dr Ibrahim Ilyasu ya ce “akwai gyare-gyare da dama Daya kamata ayiwa bangaren siyasar kasar, Wanda shi zai taka rawa wajen gyaran matsalar da kasar nan take ciki a yanzu.”

Yana mai cewa “jami’iyun siyasar da suka kwashe shekaru da dama suna bukatar a daina amfani dasu, ta hanyar sauya sababbi. Sannan shima yadda ake shiga daki bayi zaben fidda gwani shima ya kamata a mayar dashi kan tsarin kimiya.”

“Haka zalika ya kamata suma mutane su daina siyasar akida, su rinka zaben wanda ya can-canta, wanda wadannan hanyoyin kadai aka bi za’a iya rage matsalolin damukradiyar kasar nan ta ke ciki a yanzu.”

A hannu guda Wani Mai bincike a bangaren siyasa a nan Kano, Aliyu Dahiru Aliyu cewa yayi, “malamai nada tasirin wajen yin amfani da tafiyarwar addinin musulunci su samar da shuwagabanni da al’umma na gari, ta hanyar yiwa shuwagabanni nasiha, tare da fayyace mutane ire-iren mutane daya kamat su zaba a matsayi wadanda zasu mulke su.

Sakataren cibiyar samar da zaman lafiya ta Islamic centre for peace building din na kasa Khalifa Nasidi ya ce wayar da kam al’umma Kan tayar da yarzoma yayin gudanar da zaben, na daya daga cikin dalilan kafa wannan cibiyar a Afrika gaba daya.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!