Labarai
Malan Addinin musulunci na kira ga Alƙalai da su kamanta gaskiya a yayin shari’ar Kano
Gamayyar limaman masallatan juma’a da suka haɗar da ɗariƙar Tijjaniyya, Ƙadiriya, Izala da mahaddata Alqur’ani sun yi kira ga shugabanni da alƙalai da su kasance masu kamanta gaskiya a kowanne ɓangare na rayuwa domin dauwamar da zaman lafiya a faɗin kano dama ƙasa baƙi ɗaya
Sheikh Ali Ɗan Abba ne ya bayyana jim kadan bayan kammala wata bita da suka shirya kan zaburar da shugaban ni da alƙalai tabbatar da adalci musamman a wannan lokaci da ake samin ce-ce kuce akan hukuncin gwamnan a jihar kano.
Sheikh Ali Ɗan Abba ya kuma ce yana da kyau malamai su dunga anfani da mambarin su wajen faɗar gaskiya a dukkan lamari na rayuwa
Ya ƙara da cewa idan za’ayi da duba da irin yadda wannan gwamnatin Abba Kabir Yusuf ke gudanar ayyukan ta abin a yaba ne bisa yadda ta ke samar da ci gaba a faɗin jihar
Daga ƙarshe limaman da mahaddata Alqur’ani na fatan manyan shugabanni na ƙasar nan da alƙalai zasu kasan ce masu adalci wajen tabbatar da gaskiya a ko wanne ɓangare.
You must be logged in to post a comment Login