Labaran Kano
Manoma 450,000 a Kano zasu amfana da tallafin Noma
Manoma 450, 000 ne masu karamin karfi zasu amfana da tallafi na bunkasa Noma a fadin jihar Kano , ta hadin gwiwa tsakanin hukumar shirin bunkasa Noma da kiwo na jihar Kano wato Kano State Agro Pastoral Project Development, KSADP da hukumar Sasakawa ta Sasakawa Africa /SG 2000.
Shirin tallafin wanda hukumomin biyu suka sanyawa hannun na yarjejeniyar fahimtar juna da aiki tare na (MOU), zai bada tallafin a wajen Samar da iri, Taki da Feshin Gona sai lura da Gona bayan Girbi da kuma bunkasa kayan Noma da cinikin su.
Shirin zai bada horo na musamman ga ma’aikata na gona wajen koyar da bunkasa kwarewa na wanda zasu lura da duba manoma su 18,000 da masu bibiya su 440 sai mutum 220 masu samar kayan Noma da mutum 1,000 masu taimakawa manoma a cikin kauyuka da mutum 220 ma’aikatan bunkasa Noma na musamman da wasu daga cikin ma’aikatan shirin bunkasa Noma da kiwo na jiha.
Labarai masu Alaka.
Shirin Bunkasa Noma da kiwo na jihar Kano zai fara Bayen Shanu
Shirin bunkasa noma da kiwo na jiha zai hada kai da cibiyoyin bincike
Karkashin tsarin , shirin bunkasa Noma da Kiwo na jiha zai dau nauyin kudaden tafiyar da aikin na shekaru biyar, bayan mika tsare -tsare na kudade da yadda aiyyukan zasu gudana ga hukumar da zarar Sasakawa ta mika tsarin a duk shekara, wanda zai fara daga shekarar bana ta 2020, da zarar an fara Noma gadan -gadan , don bunkasa Noma da samar da wadataccen Abinci a jiha, a hannu daya da samar da aiyyukan yi tare da rage fatara da talauci a kauyuka.
Da yake jawabi mataimakin gwamnan Kano , kana babban jami’in da yake shugabantar aiwatar da shirin Nasiru Yusuf Gawuna, wanda ya saka hannu akan yarjejeniyar fahimtar tare da Mataimakin shugaba na hukumar Sasakawa Africa , Dakta Amit Roy , yace ” Kasancewar yawan al’umma da muke dasu manoma ne yasa gwamnati tayi amfani da kwarewar jami’an Sasakawa don bunkasa harkar Noma da dorewar sa ta hanyar Zamani , tare da taimakawa manoma da kayan aiki a hannu daya tare da bada horo ga jami’an aikin Noma”.
A sanarwar da kakakin shirin Aminu Kabir Yassar, ya fitar aka rabawa manema labarai, ta bayyana cewa a watan Fabrairun da ya gabata , shirin bunkasa Noma da kiwo na jiha wanda Bankin Musulunci wato Islamic Development Bank Funded Project, ke daukar nauyi tare da hadin gwiwa na tallafin kungiyar ‘Life and Livelihoods Funds ‘ aka kaddamar da shi don bunkasa Noma da samar da wadataccen Abinci mai inganci tare da rage fatara da talauci ga marasa karfi a cikin al’ummar jihar.
You must be logged in to post a comment Login