Connect with us

Labarai

Manyan hafsoshin tsaron Najeriya sun koka dangane da tara makamai domin amfani da su lokacin zabe

Published

on

Manyan hafsoshin tsaron kasar nan sun koka dangane da tara makamai da suka ce wasu ‘yan siyasar kasar nan na yi domin amfani da shi yayin babban zaben kasa da za a yi a badi.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai Magana da yawun ministan tsaron kasar nan Kanal Tukur Gusau.

Sanarwar ta ce manyan hafsoshin tsaron sun bayyana damuwar ta su ce lokacin da suke ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Asorok da ke Abuja a jiya Alhamis.

A cewar sanarwar manyan hafsoshin tsaron sun shaidawa shugaban kasar cewa, suna da bayanan sirri da suka tabbatar da cewa ‘yan siyasa na sayan makamai suna boyewa.

Haka zalika sanarwar ta kuma ruwaito manyan hafsoshin tsaron na nuna damuwa game da me yiwuwar samun rikice-rikice yayin zaben badi da kuma bayan zaben.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,749 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!