Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yan sanda  sun cafke kwamandojin yan bindiga a jihar Zamfara

Published

on

Rundunar hadakar jami’an ‘yan sanda dake karkashin ofishin Babban Sufeton ‘yan sandan  ta cafke wasu kwamandoji hudu na ‘yan bindiga a jihar Zamfara.

Kwamandojin da suka hada da Hamisu Sani, Shehu Sani, Yusuf Mande da Lawal Abubakar sun gayawa ‘yan sanda masu bincike cewa suna cikin kwamandojin ‘yan bindigar bangaren Buharin Daji.

Haka kuma zaratan ‘yan sandan dake karkashin jagorancin DCP Abba Kyari sun kuma cafke babban mai sayar da makamai ga ‘yan bindigar, wato Lawal Abubakar da yace akalla ya samar da Manyan bindigogi sama da dari ga ‘yan ta’addar.

Lawal Abubakar yace tun a baya dai marigayi Buharin daji ne ya neme shi da ya samo masa makamai inda a karon farko ya bashi Naira miliyan daya da dubu dari takwas, bayan kwana biyar Kuma Buharin dajin ya kara kiran sa ya bashi wasu Karin Naira miliyan daya da dubu dari takwas don kara samo masa wasu bindigogin inda yaje Barikin Ladi a jihar Filato ya samo su.

Yan bindigar sun ce suna daga cikin wadanda suka kokkona kauyuka da garuruwa da ma satar shanu da rakuma a sassan jihar ta Zamfara.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!